Manufofin Huxubar:

·      Kwaxaitar da mutane aljanna, da tsoratarwa daga azabar wuta.

·      Zaburarwa a kan kyawawan ayyuka.

·      Siffofin ‘yan aljanna.

·      Siffofin ‘yan wuta.

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Yaku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Yaku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammadu (r). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta".

Bayan haka: Ya ku musulmi!

Babban jigon maganarmu ta yau shi ne, magana a kan aljanna, wacce babu mai samunta sai waxanda Allah ya jiqansu daga cikin bayinsa. Ita ce babbar abar nema a wajen dukkanin musulumi baki xaya. Haqiqa ita ce babbar abar bege a wajen dukkanin muminai.

Haka kuma Allah ya yi tanadin wuta, ga dukkanin kafirai da munafukai. Allah ya halicci aljanna da ni’imominta, ya kuma halicci wuta da azabarta, kuma kowacce ya yi mata tanadin mutanenta. Allah yana cewa:

 

{وَسَارِعُوا إِلَى مَغْفِرَةٍ مِنْ رَبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا السَّمَوَاتُ وَالْأَرْضُ أُعِدَّتْ لِلْمُتَّقِينَ} [آل عمران: 133]

)Ku yi gaggawa zuwa neman gafara daga Ubangijinku da aljanna wacce faxinta ya kai faxin sama da qasa, kuma Allah ya yi tanadinta ne ga masu tsoronsa).

A wata ayar kuma, Allah Maxaukakin sarki ya qara da cewa”

 

{فَإِنْ لَمْ تَفْعَلُوا وَلَنْ تَفْعَلُوا فَاتَّقُوا النَّارَ الَّتِي وَقُودُهَا النَّاسُ وَالْحِجَارَةُ أُعِدَّتْ لِلْكَافِرِينَ} [البقرة:24 ]

(Idan kun kasa a baya, to a nan gaba ma ba za ku iya ba, ku tsoron shiga wuta wacce makamashinta mutane ne da duwatsu, an tanade ta don kafirai).

 Ya ku jamar muminai, ku sani Aljanna ita ce makomar muminai waxanda Allah ya yi musu ni’ima daga cikin annabawa da siddiqai da salihan bayi, wadda qoramunta suke gudana. Gidajenta an yi su ne da tubali na zinare da azurfa. Turvayarta daga Za’afaran ne, runfunanta an yi su ne daga lu’ulu’u. Ga mata nan zavavvu masu tarin alheri. Muminan da suka sami shiga cikinta za su ci su sha, babu bayangida, babu fitsari, babu kaki, babu zubar da yawu, ko majina. Gatsarsu qamshin almiski take..

Kullum suna cikin farin ciki da dariya, za su kasance a haka har abada. babu mutuwa, suna masu fararen fuskoki ga kyau mai matuqar burgewa, ga matan Hurun’ini. Suna cikin dangogin ni’ima waxanda ba sa yankewa. Ga kuma qari a lokacin da Ubangiji zai xauke hijabi su gan Shi, Allah Yana cewa:

 

{فَلَا تَعْلَمُ نَفْسٌ مَا أُخْفِيَ لَهُمْ مِنْ قُرَّةِ أَعْيُنٍ جَزَاءً بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ} [السجدة: 17]

(Wata rai ba ta san abin da aka voye  musu na  abin da yake faranta rai, sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa).

An karvo hadisi, daga Abu Huraira, daga manzon Allah (r) ya ce, Allah maxaukakin sarki Yana cewa: “Na yi wa bayina na qwarai alkawarin abin da ido bai tava gani ba, kunne bai tava ji ba, zuciya ba ta tava saqa shi ba”, Gaskiyar wannan shi ne faxar Allah:

 

{فَلَا تَعْلَمُ نَفْسٌ مَا أُخْفِيَ لَهُمْ مِنْ قُرَّةِ أَعْيُنٍ جَزَاءً بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ} [السجدة: 17]

 (Wata rai ba ta san abin da aka voye  musu na  abin da yake faranta rai, sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa).

Hakanan an karvo daga Abu Huraira, daga manzon Allah yana cewa: “Haqiqa farkon waxanda za su fara shiga aljanna suna farare tas kamar farin wata a ranakun hasken shi. Sannan masu biye musu, kamar tauraruwa mafi haske a sama. Ba sa fitsari, ba sa bayangida, ba sa kaki, ba sa zubar da yawu. Matajin kansu na zinariya ne. Guminsu yana qamshin almiski, turarensu na wuta na lu’ulu’u ne. Matansu kuwa Hurun’inu. Halayensu kamar halayen mutum xaya. Tsawonsu kuwa kamar tsawon babansu Annabi Adam, zira’i sittin”.

An karvo daga Jabir ya ce: Na ji manzon Allah yana cewa: “Haqiqa ‘yan aljanna suna ci, suna sha, ba sa zubar da yawu, ba sa fitsari, ba sa bayan-gida, ba sa kaki”. Sai sahabbai suka ce: to ya matsayin abincin da suke ci? Sai Manzon Allah (r) ya ce: " Gyatsa ce za su kawai, da kuma gumi, kuma gumi mai qanshin almiski. Suna tasbihi da tahmidi, kamar yadda suke numfashi. [Muslim].

An karvo daga Abi Huraira daga manzon Allah ya ce: “Duk wanda aka shigar da shi aljanna ba zai tava shiga wahala ba. Tufarsa ma ba za ta tava tsufa ba, kuma yana cikin quruciya har abada. [Muslim].

An karvo daga Abu Sa’idul Khudri da Abu Huraira, daga Manzon Allah ya ce, "Mai kira zai yi kira a ranar alqiyama, ya ce, "Ya ku ‘yan aljanna, haka za ku dawwama cikin qoshin lafiya, babu cuta har abada, kuma zaku dawwama a cikin rayuwa babu mutuwa ha abada. Za ku dawwama a cikin quruciya babu tsufa har abada. Kuma za ku dawwama a cikin ni’ima babu talauci har abada”. Wannan ya yi daidai da faxin Allah maxaukakin sarki cewa:

 

{وَنُودُوا أَنْ تِلْكُمُ الْجَنَّةُ أُورِثْتُمُوهَا بِمَا كُنْتُمْ تَعْمَلُونَ} [الأعراف: 43]

(Kuma aka kira ‘yan aljanna aka ce dasu " Wannan gidan aljanna ne, an gadar muku da ita sakamakon abin da kuka kasance kuna aikatawa).[Muslim].

An karvo daga Abdullahi xan Qais, daga Manzon Allah ya ce: “Haqiqa mumini yana da wata rumfa a gidan aljanna wacce aka yi ta daga gudan lu'ulu'u mai kwarmi. tsawonta ya kai Mil sittin. Kowane mumini an tanadar masa iyalansa.Yana ziyartarsu, kuma ba sa ganin junansu. [Muslim].

Haka nan an karvo daga Abu Huraira ya ce: Manzon Allah ya faxa cewa: “Saihanu da Juhainu da Furat da Nil, duksuna daga cikin qoramun aljanna suke.” [Muslim].

Amma ita kuwa wuta, gida ne na bala’i da azaba. Ana shayar da ‘yan cikinta daga tafasasshen ruwan zafi. Allah ya ce:

 

{شَرَابٌ مِنْ حَمِيمٍ وَعَذَابٌ أَلِيمٌ بِمَا كَانُوا يَكْفُرُونَ} [يونس: 4]

(Suna wani abin sha na tafasasshen ruwa , da wata azaba mai raxaxi saboda abin da suka kasance suna aikatawa na kafirci).

 Wuta makoma ce mai munin gaske ga duk bayi masu savo. Allah ta'ala ya ce:

 

{هَذَا وَإِنَّ لِلطَّاغِينَ لَشَرَّ مَآَبٍ*جَهَنَّمَ يَصْلَوْنَهَا فَبِئْسَ الْمِهَادُ} [ص: 55-56]

 (Lalle waxanda suka wuce iyaka suna da mafi mummunar makoma. Jahannama ce da za su shege ta. To tir da wannan abin shimfixar).

Allah zai sanya musu wando na dalmar wuta, sannan wutar za ta lulluve fuskokinsu baki xaya. Allah yana cewa:

 

{سَرَابِيلُهُمْ مِنْ قَطِرَانٍ وَتَغْشَى وُجُوهَهُمُ النَّارُ} [إبراهيم: 50]

 (Wandunansu na dalmar wuta ne, sannan wutar za ta lulluve fuskokinsu).

An karvo daga Shaqiq xan Abdullahi, ya ce, Manzon Allah ya faxa cewa: “Za a zo da jahannama a ranar alqiyama, tana da linzami dubu saba’in, tare da kowane linzami akwai mala’ika dubu saba’in suna janta” [Muslim].

An karvo daga Abu Huraira, ya ce, Manzon Allah (r)  ya ce: "Wutar da mutane suke amfani da ita vangare xaya ne daga cikin vangarori saba'in na zafin wutar jahannama”.Sai sahabbai suka ce: "Ai ya manzon Allah ko da kamar haka take ai ta isa ta zama azaba". Sai ya ce, "To an fifita ta lahira da kaso sittin da tara sama da ta duniya kowane kaso zafinsa ya kai zafin ta duniya". [Muslim].

An karvo daga Abu Huraira yana cewa: wani lokaci muna tare da Manzon Allah, sai ya ji wata qara, sai Manzon Allah ya ce, "Kun san ko qarar mene ne wannan? Sai muka ce, "Allah da manzonsa ne suka fi kowa sani". Sai ya ce, "Wani dutse ne da aka jefa shi a wuta tsawon shekara saba’in sai yanzu ya iske qarshenta. [Muslim ne ya rawaito shi].

An karvo daga Samurah. Ya ji Manzon Allah  yana cewa: "Daga cikin mutane akwai wanda wuta za ta kama shi har zuwa idon sawusa. Wani kuma zuwa qug. Wani kuma zuwa wuyansa”. [Muslim ne ya rawaito shi].

Allah ka samu cikin masu rabauta da gidan aljannah. Ka haxa da annabawa da siddiqar, da shu'hada'u da salihan bayinka a cikita. Ka sauqaqe mana aikin da za kusantar da mu zuwa gareta. Ka tsare daga azabar wuta. Abin da ya sauwaqa ku ji shi ke nan daga bakina. Ina neman gafarar Allah ga ni kaina da ku baki-xaya. Don haka kuma ku nemi gafarsa, donmin shi mai gafara ne mai jin-qai.

 

Yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su tabbata ga annabin rahama, annabinmu Muhammadu da alayensa da sahabbansa da waxanda suka bi tafarkinsa har zuwa tashin qiyama. Bayan haka:

Ya ku bayin Allah. Ubangiji mai girma da buwaya ya horewa bayin hanyoyi daban daban don samin gidan aljannah domin tsananin tausayinsa ga bayinsa.

Allah yana faxa a cikin littafin mai tsarki cewa:

 

{إِنَّ اللَّهَ اشْتَرَى مِنَ الْمُؤْمِنِينَ أَنْفُسَهُمْ وَأَمْوَالَهُمْ بِأَنَّ لَهُمُ الْجَنَّةَ يُقَاتِلُونَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ فَيَقْتُلُونَ وَيُقْتَلُونَ وَعْدًا عَلَيْهِ حَقًّا فِي التَّوْرَاةِ وَالْإِنْجِيلِ وَالْقُرْآَنِ وَمَنْ أَوْفَى بِعَهْدِهِ مِنَ اللَّهِ فَاسْتَبْشِرُوا بِبَيْعِكُمُ الَّذِي بَايَعْتُمْ بِهِ وَذَلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ} [التوبة: 111]

 (Lalle Allah ya sayi rayukan muminai da farashin aljanna. Su yi yaqi don xaukaka kalmar Allah, sai su kashe kuma a kashe su. Wannan alkawari ne na gaskiya da ya xaukarwa kansa a cikin Attaurah da Linjila da Alqur'ani. Wanene wanda ya fi Allah cika alkawarinsa?! Don hka ku yi murna da wannan ciniki da kuka yi da Allah. Wannan kuma shi ne babban rabo

An karvo daga Jarir xan Abdullahi ya ce: Mun kasance a wani lokaci a wajen Manzon Allah da daddare, wata yana tsakiyar haskensa, sai Manzon Allah ya ce: “Haqiqa za ku ga Ubangijinku, a fili kamar yadda kuke ganin wannan watan a wannan lokaci, ta bare da turereniya  ba. Saboda haka duk kada xayanku ya yarda a fi qarfinsa akan sallar Asuba da ta Magariba". [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Manzon Allah ya ce: “Duk wanda ya yi sallar nafila raka’a goma sha biyu a yini da dare, Allah zai gina masa gida a aljanna. Raka’a biyu kafin asubahi. Raka’a huxu kafin azahar da raka’a biyu a bayanta, da raka’a biyu bayan sallar magariba da raka’a biyu bayan sallar isha’i". Muslim ne ya ruwaito shi.

A game da qiyamullaili, Allah yana cewa;

 

{تَتَجَافَى جُنُوبُهُمْ عَنِ الْمَضَاجِعِ يَدْعُونَ رَبَّهُمْ خَوْفًا وَطَمَعًا وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنْفِقُونَ} [السجدة: 16]

(Jukkunansu suna nisa da shimfixinsu. Suna bautawa Ubangijinsu suna masu tsoron azabarsa, masu kwaxayin ladansa. Kuma suna ciyarwa daga abin da muka azurta su). Shi ya sa Manzon Allah yake cewa: “Ku yaxa sallama a tsakaninku. ku ciyar da abinci,  ku sada zumunci, ku yi sallah da daddare lokacin da mutane suke barci, sai ku shiga aljanna da aminci". [Tirmizi ne ya ruwaito].

Sannan ka lizimci ambaton Allah. Kamar yadda Annabi (r) yake cewa: (Wanda duk ya ce, Subhanallahi, wal-Hamdu lillahi, to za a dasa masa dabino a aljannah). (Tirmizi ne ya ruwaito).

Hakanan Manzon Allah yana cewa: “Na ga Annabi Ibrahim a daren da aka yi Isra’i da ni. Ya ce ya Muhammad ka isar wa da al’ummarka gaisuwata. Ka ba su labari da cewa, aljanna turvayarta mai qanshi ce. Ruwanta mai daxi ne. qasarta qequwa ce. Dashenta kuwa shi ne, Subhanallahi, wal-Hamdu lillahi Walaa-ilaaha Illal-Lahu. Wal-Lahu Akbar". [Tirmizi ne ya ruwaito].

Yana daga cikin hanyoyin samin gidan aljannah, bawa ya kyautata halayensa. Manzon Allah (r) yana cewa: "Ba na ba ku labari ‘yan aljanna daga cikin mazajenku ba? Annabi yana aljanna, Siddiqi yana aljanna, Shahidi yana aljanna, da wanda yake ziyarar xan’uwansa a can wani gari don Allah. Matanku 'yan aljannah su ne: Da dukkanin mace mai yawan nuna qauna ga mijinta, mai yawan haihuwa, wacce take xora hannunta a kan hannun mijinta in ta vata masa rai, ta riqa cewa, "Ba zan iya barci ba idan ba ka huce ba". Nisa'i ne ya ruwaito shi.

Allah maxaukakin sarki yana cewa:

 

{إِنَّ الَّذِينَ آَمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ أُولَئِكَ هُمْ خَيْرُ الْبَرِيَّةِ*جَزَاؤُهُمْ عِنْدَ رَبِّهِمْ جَنَّاتُ عَدْنٍ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ ذَلِكَ لِمَنْ خَشِيَ رَبَّهُ} [البينة: 7-8]

(Haqiqa waxanda suka yi imani, kuma suka yi ayyuka na gari, to waxannan su ne mafi alkhairin halitta. Sakamakonsu a wajen Ubangijinsu aljannatai ne waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu. Suna dawwama a cikinsu har abada. Allah ya yarda da su. Suma sun yarda da shi. Wannan sakamakon ne na wanda duk ya ji tsoron Ubangijinsa).

Ya Allah ka ba mu da cewa da gidan Aljannarka ta Firdausi. Ka sanya mu cikin masu aiki tuquru don gina lahirarsu da sa mun yardarka, da ganin fuskarka ranar gobe qiyama. Allah ka nisatar da fuskokinmu daga wuta. Ka nesatar da ayyukanmu daga ayyukan 'yan wuta. Ka sa aljannarka madawwamarmu. Amin.


 • Gargadi Akan bidia
 • Rayuwar Lahira Itace Rayuwa Ta Haqiqa
 • Jan- Kunne Kan Bokaye Da Matsafa
 • Imani da sunayen Allah kyawawa, tare da sharhin wasu daga cikinsu.
 • Imani Da Qaddara
 • Addua muhimmancinta da sharadanta
 • Alamomin Tashin Qiyama
 • Amfanin Tsoron Allah A Rayuwar Musulmi
 • Wuta Da Aljanna
 • Wasu Daga Cikin Ayoyin Halittun Allah
 • Falalar Wanda Ya Tabbatar Da Tauhidi
 • Yin Aiki Don Allah Da Bayanin Muhimmancin sa
 • Lazimtar Sunnar Annabi s.a.w
 • Dogaro Ga Allah
 • Tsoro Tare Da Kyakkyawan Fata
 • Son Allah Da Manzonsa, Da Qaddamar Da Su Akan Waninsu
 • Daidaito akan koyarwar alqurani da sunnah
 • Rayuwa bayan mutuwa

aika mana da email xinka domin saquna da xumixuminsu su riske ka

jinsi
gari (qasa)
email