Tawakkali ga Allah madaukakin sarki babban abin buqata ne daga bawa, kuma umarni ne daga Allah ga bayinsa muminai, ya umarce su da haka a cikin kowane yanayi . Sannan maanar tawakkali shine natsuwar zuciya wajen dogaro ga Allah don samun abubuwan amfani ko tunkude sharri.
Bayan haka: Ya bayin Allah! Haqiqa musulunci addni ne da yake da nagartattun 'dabi’u, don haka ya dace da 'dabi’un da ba a gur'bata su ba. Ya kuma dace da 'dabi’un da suke masu kyawu. Musulunci shi ne maganin gur'batattun 'dabi’u
Ilimi haske ne da shiriya, kamar yadda jahilci duhu ne da bata. Ilimi idan ya hadu da imani, daukaka ne duniya da lahira, kuma aiki shine ribar ilimi, kuma shine asasin ilima da gayar sa, don haka ya wajaba ga daliban ilimi yin aiki da iliminsu, in ba haka ba kuwa, sai ilimin ya zama hasara gare su kuma mara amfani,domin malamin da baya aiki da ilimin shi, kamar fitila ce haska wani kona kanki.
Haqiqa jin qai da rahama siffofine guda biyu daga cikin siffofin Ubangiji maxaukaki, kuma sunayene daga cikin sunayensa mafiya kyau, shi yasa ya siffantu dasu, kuma ya umarci bayinsa da siffantuwa dasu, domin samar da tausayi da rangwame tsakaninsu.
aika mana da email xinka domin saquna da xumixuminsu su riske ka